Hatsarin jirgin sama ya kashe mutum biyu a Ghana

Mutane biyu ne suka mutu bayan wani ƙaramin jirgin sama ya yi hatsari tare da kamawa da wuta a yankin Tema Community One da ke Greater Accra a ƙasar Ghana ranar Litinin. Rahotanni sun ce jirgin ya fara kamawa da wuta ne kafin ya faɗi a filin wasa na wata makaranta kusa da cibiyar renon […]

Newstimehub

Newstimehub

18 Mar, 2026

mini 8409 mutum biyu sun mutu a ghana sanadin hatsarin jirgin sama

Mutane biyu ne suka mutu bayan wani ƙaramin jirgin sama ya yi hatsari tare da kamawa da wuta a yankin Tema Community One da ke Greater Accra a ƙasar Ghana ranar Litinin.

Rahotanni sun ce jirgin ya fara kamawa da wuta ne kafin ya faɗi a filin wasa na wata makaranta kusa da cibiyar renon yara, lamarin da ya janyo tashin gobara mai ƙarfi.

Jami’an ’yansanda da na kashe gobara sun isa wurin cikin gaggawa, inda suka shawo kan wutar tare da killace yankin domin tabbatar da tsaro.

Hukumomi sun ce an kwashe malamai da ɗalibai daga makarantar da ke kusa da wurin kafin hatsarin, wanda hakan ya hana asarar rayuka daga ɓangaren yara.

Ana sa ran fara cikakken bincike domin gano musabbabin hatsarin, yayin da masu bincike ke shirin tattara tarkacen jirgin domin yin nazari.

Tushen labari: Newstimehub