Aƙalla mutum 23 ne suka mutu yayin da sama da mutum 100 suka jikkata sakamakon hare-haren ƙunar-baƙin-wake da suka auku a birnin Maiduguri, Jihar Borno a daren Litinin, kamar yadda hukumomi suka tabbatar.
Hare-haren sun faru ne a wurare daban-daban da suka haɗa da ƙofar Asibitin Koyarwa na Jami’ar Maiduguri, Monday Market da kuma wani gidan waya, lamarin da ya janyo asarar rayuka da raunuka masu yawa.
Hukumar agajin gaggawa ta NEMA ta ce da dama daga cikin waɗanda suka jikkata na karɓar magani a asibitoci daban-daban a birnin, yayin da jami’an tsaro ke ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin.
Mazauna yankin sun bayyana cewa lamarin ya tayar musu da hankali, suna mai cewa birnin ya fara komawa yanayin tashin hankali bayan shekaru na samun sauƙi.
‘Yansanda sun ce ana zargin hare-haren ƙunar-baƙin-wake ne suka haddasa fashewar, tare da kira ga jama’a da su riƙa kai rahoton duk wani abu da ba su yarda da shi ba domin ƙarfafa tsaro.
Tushen labari: Newstimehub














