Gwamnatin Nijeriya ta gabatar da mutum 128 da aka ceto daga hannun ‘yan bindiga a jihar Zamfara

Babban Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Harkokin Tsaro Mallam Nuhu Ribadu ne ya gabatar da mutanen da aka ceto ɗin ga manema labarai a ofishinsa da ke Abuja a ranar Talata.

Newstimehub

Newstimehub

26 Aug, 2025

4c433526cd6bbacacc1ab87ece02ff504dddf378947b3e6c900fa0bb4e4c8fa1 main

Gwamnatin Nijeriya ta yi nasarar kubutar da mutum 128 daga hannun ‘yan bindiga a Kaura Namoda da ke jihar Zamfara.

Babban Mai Baiwa Shugaban Ƙasa Shawara kan Harkokin Tsaro Mallam Nuhu Ribadu ne ya gabatar da mutanen da aka ceto ɗin ga manema labarai a ofishinsa da ke Abuja a ranar Talata.

A cewar Ribadu, aikin ceton ya nuna sabbin dabarun tsaron kasa da kuma irin namijin kokarin da jami’an tsaro ke yi.

Ya ce za a kula da lafiyar mutanen da aka ceto da kuma ba su tallafi don komawa cikin iyalansu da al’ummominsu.

Ribadu ya yaba da jarumtaka da ƙwarewarsojoji, ‘yan sanda, jami’an leken asiri, da sauran hukumomin da suka yi aikin ceton.

Ya kuma yi kira ga ‘yan Nijeriya da su tallafa wa jami’an tsaro da bayanan da suka dace domin yaƙar ‘yan fashi da ta’addanci.