Gwamnan jihar Abba Kabir Yusuf ya ƙaddamar da Majalisar Shura, a matsayin wani sabon kwamiti don jagoranta da ba da shawarwari kan al’amuran da suka addini da zamantakewa da ke shafar ‘yan jihar.
Da yake jawabi a yayin bikin kaddamarwar a gidan gwamnati, Gwamnan ya bayyana majalisar a matsayin wani muhimmin ginshiki na kokarin gwamnatinsa na tabbatar da adalci, gaskiya, da haɗin kai a harkokin mulki.
A cewarsa, Majalisar Shura za ta taka muhimmiyar rawa wajen bayar da shawarwari kan harkokin addini da na jama’a tare da tabbatar da cewa ana jin muryoyin ‘yan kasa wajen yanke shawara.
“Manufar wannan gwamnati ita ce tabbatar da cewa mutane sun shiga cikin harkokin mulki. Muna son ‘yan jiharmu su ba da gudunmawar ra’ayoyinsu da shawarwari don ci gaban jihar baki daya.”