Gwamnatin ƙasar Ghana ta ƙara farashin da ya manoman ƙasar za su sayar da ton ɗin koko daga dala $3,100 zuwa dala $5,040.
Kamfanin dillancin labaran ƙasar ya ruwaito cewa wannan sabon farashin zai fara aiki ne daga ranar 7 ga watan Agustan shekarar 2025.
Ministan Kuɗin Ƙasar, Dakta Cassiel Ato Forson, da ya jagorancin zaman kwamitin daidaita farashin kokon a Accra ranar Litinin, ya ce sabon farashin ya dace da alƙawarin da Shugaba John Mahama ya yi wa manoman kokon na tabbatar da cewa farashin koko ya kai kashi 70 cikin 100 farashin da masu saye daga ƙetare ke biya.
Ya ƙara da cewa farashin tun da farashin da ake sayen kokon a ƙetare da kudin dakon dala $7, 200, shi ya sa gwamnatin ta ƙara wa manoman farashin da za su yi ta sayar da ko wane ton da kokonsu.
Ministan Kudin ya bayyana cewa wannan matakin ya saɓa wa matakin da gwamnatin da ta shuɗe ta ɗauka inda ta ƙayyade farashin masu saye daga ƙetare kan kuɗi dala $4,850 ga ko wane ton, inda ta ƙayyade wa manoma sayar da ko wane tan na koko kan kuɗi dala $3,100, wanda kashi 63.9 cikin 100 ne na farashin da ake sayen kokon daga ƙetare, duk da cewa farashin kokon a kasuwar duniya ya haura hakan.