Isra’ila na karya yarjejeniyar tsagaita wuta a Lebanon, ta ci gaba da kai hari

A harin baya bayan da ta kai, Isra’ila ta ci gaba da karya yarjejeniyar tsagaita wuta a kudancin Lebanon inda ta kashe mutum guda da jikkata wasu mutanen biyu.
27 Jan, 2026
Manyan jami’an China sun tattauna da Ƙungiyar OIC a yanayin da rikicin Gabas ta Tsakiya ke ƙara muni

Mataimakin shugaban ƙasar China da ministan harkokin wajen ƙasar sun gana da babban sakataren ƙungiyar haɗin kan ƙasashen musulmi ta OIC, inda suka yi kira da a samar da haɗin gwiwa a fannin tsaron yankin yayin da rikicin Amurka da Iran ke ƙara muni.
26 Jan, 2026
Yaƙin da ake yi da ta’addancin Daesh yana ƙara ƙarfi: Erdogan

Shugaban Turkiyya ya ce kawar da ta’addancin ‘yan a-aware da ke barazana ga arewacin Syria zai kawo sauƙi ga ɗaukacin yankin.
25 Jan, 2026
Iran ta gargaɗi Amurka: ‘Za mu ɗauki kowane irin hari a matsayin cikakken yaƙi a kanmu’

Iran ta ce ba za ta bambance tsakanin ƙaramin hari ko babban hari ba inda ta ce idan Amurka ta kai mata hari za ta mayar mata da martani mai ƙarfi.
24 Jan, 2026

Turkiyya ba ta goyon bayan tsoma bakin ƙasashe waje a kan Iran – Erdogan

Adadin mutanen da suka mutu a zanga-zangar Iran ya kai 4,000: Rahoto

Iran ta sha alwashin gwabza yaƙi da duk ƙasar da ta yi gangancin kai wa Khamenei hari

Syria ta ayyana harshen Kurdanci a matsayin ‘harshen ƙasa’, sannan ta ba Kurdawa haƙƙin ‘yan ƙasa

Ministan Wajen Saudiyya da takwarorinsa na Iran, Oman da Qatar sun tattauna kan zaman lafiyar yanki
14 Jan, 2026
Trump ya yi barazanar ‘ɗaukar tsattsauran mataki’ idan Iran ta rataye masu zanga-zanga
Iran ta ce ‘wasan kwaikwayon’ da Washington ke yi zai sake yin rashin nasara.

13 Jan, 2026
‘Taimako yana zuwa’ in ji Trump ga masu zanga-zanga a Iran
A wani rubutu Trump ya ce: “Na soke dukkan ganawar da zan yi da jami’an Iran har sai an daina kai wa masu zanga-zanga hari. Taimako na kan hanyarsa. MIGA!!!”

12 Jan, 2026
Iran ta ce a ‘shirye’ take ta tattauna da Amurka amma kuma ta ‘shirya wa yaƙi’
Ministan Harkokin Wajen Iran Abbas Araghchi a ranar Litinin ya bayyana cewa Iran ba ta neman yaƙi amma ta shirya domin ta kare kanta.

10 Jan, 2026
Kungiyar ta’addanci ta YPG ta ƙwace iko da wani asibiti a Aleppo, ta kori ma’aikatan lafiya
Ƙungiyar ta’addanci ta YPG ta mayar da asibitin Yassin da ke unguwar Sheikh Maqsoud zuwa wani sansani domin ƙarfafa kansu, kamar yadda Kamfanin Dillancin Labarai na Larabawa na Syria ya ambato ma’aikatar lafiya ta ƙasar tana bayar da tabbaci.

9 Jan, 2026
Ma’aikatar Tsaron Syria ta sanar da tsagaita wuta a wasu unguwannin Aleppo
Ma’aikatar tsaron Syria ta ce ‘yan bindiga suna da zuwa ƙarfe 9 na safe su bar unguwannin da ake rikici da su.

2 Jan, 2026
Rundunar hadakar soji da Saudi ke jagoranta ta kai hari kan ‘yan-awaren da UAE ke goyon baya a Yemen
Rundunar hadakar soji da Saudiyya ke jagoranta ta kai hari kan ‘yan-awaren STC da UAE ke goyon baya a Yemen

2 Jan, 2026
Turkiyya da wasu ƙasashe bakwai suna matsa wa Isra’ila lamba don ɗage takunkuman hana Gaza tallafi
Ministocin sun yaba da kokarin hukumomin Majalisar Dinkin Duniya, musamman UNRWA, da kuma kungiyoyin agaji na kasa da kasa, saboda ci gaba da bayar da agaji a karkashin abin da suka bayyana a matsayin yanayi mai matukar wahala da rikitarwa.

30 Dec, 2025
Trump ya ce Hamas za ta “ɗanɗana kuɗarta” idan nan da ɗan lokaci ba ta ajiye makamai ba
Trump na goyon bayan Netanyahu kan tattaunawa game da Gaza, amma ya ce Amurka da Isra’ila ba su cim ma yarjejeniya game da Gaɓar Yamma ba a yayin da ake matsa lamba kan tsagaita wuta.

29 Dec, 2025
Hamas ta ce harin Isra’ila ya kashe babban mai magana da yawunta a lokutan yaƙi, Abu Ubaida
Abu Ubaida da kulluma fuskarsa ke rufe kuma ba kasafai ake ganinsa a bainar jama’a ba, shi ne wanda aka fi jin muryarsa a duk tsawon lokacin da aka shafe ana yaƙi, inda yake yawan aika saƙonnin da ke isa ga al’ummar duniya.

29 Dec, 2025
Ministan Tsaron Ƙasa na Isra’ila na so a hana kiran sallah a masallatan ƙasar
Falasɗinawa mazauna Isra’ila sun yi watsi da batun, suna cewa abu ne da ke sake neman taɓa mutunci da asali da kuma tunzura mutane su yi ƙiyayya wa addini.

