‘Yar tseren gudu daga Ethiopia, Fotyen Tesfay, ta nuna bajinta a gasar Barcelona Marathon bayan ta lashe gasar da lokaci na biyu mafi sauri da aka taɓa samu a tarihin marathon. Wannan shi ne karo na farko da ‘yar gudun mai shekaru 28 ta shiga gasar marathon.
Tesfay ta kammala tseren cikin sa’o’i 2 da mintuna 10 da sakan 53, inda ta bar abokiyar takararta Jepkosgei Kiplimo a matsayi na biyu da kusan mintuna takwas a baya, yayin da Zeineba Yimer ta zo ta uku.
Ta bayyana cewa burinta shi ne ta karya tarihin duniya, amma iska mai ƙarfi ta sa ya zama da wahala ta ci gaba da gudun da take yi a ƙarshen tseren. Lokacin da ta yi ya rage da sakan 57 kacal kafin kai wa tarihin duniya na awa 2:09:56 da Ruth Chepng’etich ta kafa.
A bangaren maza kuwa, Abel Chelangat daga Uganda ne ya lashe gasar, inda ya doke Patrick Mosin da Jonathan Korir. Tesfay ta ce tana da niyyar sake gwada sa’arta domin karya tarihin duniya a wata marathon nan gaba.














