Faransa ta zama ƙasa ta farko daga Tarayyar Turai da ta sanya hannu kan yarjejeniyar ba da damar aika sojoji ziyara tsakanin ta da Philippines. Ma’aikatar tsaron Philippines ta bayyana cewa an rattaba hannu kan yarjejeniyar ne a birnin Paris ranar Alhamis tsakanin sakataren tsaron ƙasar, Gilberto Teodoro Jr., da ministar rundunar sojin Faransa, Catherine Vautrin.
Yarjejeniyar, wadda ake kira Agreement on the Status of Visiting Forces (SOVFA), za ta ba kasashen biyu damar tura jami’an sojinsu zuwa ƙasashen juna tare da faɗaɗa haɗin gwiwar tsaro. Hukumomin Philippines sun ce wannan takarda za ta zama ginshiƙi wajen sauƙaƙa sabbin ayyukan haɗin gwiwar soja tsakanin rundunonin ƙasashen biyu a yankunan kowannensu.
Ko da yake Faransa ita ce ƙasa ta farko daga EU da ta cimma irin wannan yarjejeniya da Philippines, ita ce ta shida gaba ɗaya da ta yi hakan. Amurka ce ta fara kulla irin wannan yarjejeniya da Manila a 1998, sai Australia a 2007, Japan a 2024, sannan New Zealand da Canada a bara.













