Emine Erdogan ta yi kira ga ƙarfafa haɗin kan al’adu da muhalli a wajen taron SCO

Matan shugabannin kasashen Turkiyya, Nepal, Armenia, Malaysia, Mongolia, Azerbaijan, Iran, Masar da Uzbekistan, tare da ‘yar shugaban kasar Iran, sun halarci taron raya al’adu a gefen taron SCO.

Newstimehub

Newstimehub

2 Sep, 2025

6147553882b29d2735173de00fb0fdccf80247f052bf120df9c622815a1b80f7

Uwargidan shugaban kasar Turkiyya Emine Erdogan ta halarci wani shirin raya al’adu wanda uwargidan shugaban kasar China Peng Liyuan ta shirya a gefen taron shugabannin kasashen kungiyar SCO karo na 25.

Sanarwar da fadar shugaban kasar Turkiyya ta fitar a ranar Litinin din nan ta ce, Peng ta yi kyakkyawar tarba ga Erdogan a wajen taron, inda ta kuma hadu da matan shugabannin kasashe don daukar hoto kafin halartar taron raya al’adun wanda ke nuna al’adun kasashen da ke halartar taron.

Haka kuma matan shugabannin kasashen Nepal, Armenia, Malaysia, Mongolia, Azerbaijan, Iran, Masar da Uzbekistan, tare da ‘yar shugaban kasar Iran ma sun halarci taron.

2e57b4275d4e1c7c1f554e5040e4a341783813fd0ecfc283923312d2c60c150d

Taron ya bayar da dama ga mahalartan wajen yin musayar ra’ayoyi kan al’du da kyawawan abubuwan da suke da shi na bai daya, in ji sanarwar.

Bayan taron, Emine Erdogan ta fitar da sako ta shafin sadarwa na yanar gizo tana mai bayyana jin dadinta bisa halartar taron da Peng ta karbi bakunci.