Dakarun rundunar Rapid Support Forces (RSF) sun yi luguden wuta a wani sansanin ‘yan gudun hijira da ke yankin Darfur da ke yammacin Sudan, inda suka kashe aƙalla mutum 3, cikinsu har da ƙananan yara da wata mace mai juna biyu, a cewar wata ƙungiyar bayar da agaji ta likitoci.
Kazalika luguden wutar da dakarun Rapid Support Forces suka yi sansanin Abu Shouk da ke kusa da Al Fasher, babban birnin lardin North Darfur, ya yi sanadin jikkatar mutum 13, a ceewar ƙungiyar likitoci ta Sudan Doctors Network a wata sanarwa da ta fitar.
Luguden wutar da dakarun suka yi ranar Asabar shi ne irinsa na biyu da suka kai hari a sansanin a ƙasa da mako ɗaya.
Ƙungiyar Resistance Committees da ke Al Fasher, wadda ke bibiyar yaƙin da ke faruwa a yankin, ta ce dakarun RSF sun kwashe awanni da dama suna “lguden wuta babu ƙaƙƙautawa” tun da sanyin safiya. A wani saƙo da ta wallafa a shafinta na Facebook ta ce dakarun sun kuma lalata wurare da dama da ke sansanin da ma yankunan da ke maƙwabtaka da shi.