Dai Qisheng: Nijeriya ta tasa ƙeyar ƙasurgumin ɗan daba da ake nema ruwa-a-jallo a China

Mista Dai Qisheng ƙasurgumin shugaban ‘yan daba ne da ake nema ruwa-a-jallo a China.

Newstimehub

Newstimehub

25 Aug, 2025

da83c9da6267a11ba02e051be1398b1ba8fd750b9a4ee425203d85d7222b1fa9

Rundunar ‘yan sandan Nijeriya ta yi shelar kamawa tare da tase ƙeyar ƙasurgumin shugaban ‘yan daba da ake nema ruwa-a-jallo, Mista Dai Qisheng, zuwa ƙasarsa, China.

Wata sanarwa da rundunar ta wallafa a shafinta na Facebook ranar Lahadi ta ce ta samu wannan nasarar ce sakamakon haɗa gwiwa da ofishin rundunar ‘yan sanda ta ƙasa da ƙasa da ke Abuja tare da rundunar ‘yan sanda ta ƙasa da ƙasa da ke Beijing da kuma ofishin jakadancin China a Nijeriya.

Sanarwar, wadda jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan ƙasar, Olumuyiwa Adejobi, ya sanya wa hannu ta ce ana neman Mista Dai Qisheng ne a lardin Guizhou na ƙasar China bisa zargin shiryawa tare da jagorantar aikata laifi na kai hari da kuma tserewa daga ƙasarsa bayan ofishin tsaro na ƙaramar hukumar Zhijin ya ba da sammacin kamo shi a shekarar 2024.

Bayan Mista Dai Qisheng ya tsere Nijeriya domin neman mafaka, sanarwar ta ce jami’an cibiyar ‘yan sanda ta ƙasa da ƙasa da ke Abuja sun kamo shi ranar 8 ga watan Agusta.