Boko Haram: Sojojin Saman Nijeriya ‘sun kashe ‘yan ta’adda 592’ a Borno cikin wata takwas

Rundunar ta ce hare-haren, waɗanda suka ƙunshi tashin jiragen yaƙi sau 798, sun yi nasarar rage ƙarfin mayaƙan ISWAP da Boko Haram sosai a arewa maso gabashin Nijeriya.

Newstimehub

Newstimehub

13 Aug, 2025

ac3286a4905eee2c46d81eb23b15cb6a9b89f909670fccd809564d98b9b33e8c

Rundunar sojin saman Nijeriya ta ce ta shafe sa’o’i 1,500 tana kai harin sama a Jihar Borno da ke arewa maso gabashin ƙasar cikin watanni takwas da suka gabata inda ta kashe ‘yan ta’adda 592 tare da lalata kayayyakin abokan gaban 372.

Rundunar ta ce hare-haren, waɗanda suka ƙunshi tashin jiragen yaƙi sau 798, sun yi nasarar rage ƙarfin mayaƙan ISWAP da Boko Haram sosai a arewa maso gabashin Nijeriya.

Mai magana da yawun rundunar, Air Commodore Ehimen Ejodame, a wata sanar da ya fitar ranar Talata, ya ce babban hafsan sojin saman Nijeriya, Air Marshal Hasan Abubakar, shi ya bayyana alƙaluman a lokacin da ya kai ziyarar ban girma ga gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Zulum, a birnin Maiduguri.

“Rundunar Sojin Saman Nijeriya ta ƙaddamar da hare-hare babu ƙaƙƙautawa kan ‘yan ta’adda a arewa maso gabashin Nijeriya, inda [muka] kashe aƙalla mayaƙa 592 tare da shafe kayayyakin abokan gaba 372 cikin watanni takwas — wani yanayin aikin da a halin yanzu ya fara zarce ayyukan da muka yi gaba ɗaya a shekarar 2024,” in ji babban hafsan sojin saman.

“Da taimakon ingantattun jiragen sama da kuma ikon iya kai hari a duk inda muke so ba tare da samun kuskure ba, mun kassara ikon zirga-zirgar ‘yan ta’addan ta hanyar lalata motocinsu 206 da kuma muhimman wuraren haɗa abubuwan fashewa 166 na abokan gaba. A wannan shekarar, yaƙinmu na sama ya fi sauri da kuma yin sara a kan kan gaɓa. Muna kashe muhimman ‘yan ta’adda da kuma lalata ababen zirg-zirgansu tare da farautar duk masu barazana ga zaman lafiya a arewa maso gabashin Nijeriya,” a cewarsa.

Daga Gonori zuwa Rann da Dikwa zuwa Damboa da kuma Azir zuwa Mallam Fatori, Abubakar ya ce jiragen rundunar sojin saman suna cigaba da kai hare-hare babu dare babu rana ta hanyar amfani da jiragen yaƙi ba tare da kuskure ba.