Babban Hafsan Hafsoshin Tsaron Nijeriya, Janar Christopher Musa, ya yi maraba da hukuncin da wata kotu a kasar Finland ta yanke wa mai fafutukar kafa kasar Biafra, Simon Ekpa, inda ya ce masu daukar nauyin ta’addanci za su fuskanci hukunci, ba tare da la’akari da inda suke ba.
Kotun gundumar Päijät-Häme da ke birnin Lahti na kasar Finland ta yanke wa Ekpa hukuncin daurin shekaru shida a gidan yari bisa samun sa da laifin ta’addanci.
Kotun ta samu Ekpa da laifin shiga ayyukan ta’addanci.
A cewar mai gabatar da ƙara, laifukan sun shafi ayyukansa na sake kafa kasa mai cin gashin kanta a yankin Biafara na Nijeriya.
Jim kadan bayan yanke hukuncin, Janar Musa ya bayyana hukuncin a matsayin wata gagarumar nasara a yakin da duniya ke yi da ta’addanci da tsattsauran ra’ayi.
An bayyana hakan a wata sanarwa da Daraktan yada labarai na rundunar, Birgediya Janar Tukur Gusau ya fitar.