Fiye da mutane 40 ne suka ɓace bayan wani kwale-kwale ɗauke da fasinjoji aƙalla 50 ya kife a Jihar Sokoto da ke arewa maso yammacin Nijeriya, kamar yadda Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Ƙasa (NEMA) ta bayyana.
“An ceto kusan mutane 10, yayin da fiye da fasinjoji 40 suka ɓace,” a cewar wata sanarwar da NEMA ta fitar a ranar Lahadi.
Rahotanni sun bayyana cewa waɗanda lamarin ya rutsa da su na kan hanyarsu ta zuwa kasuwar Goronyo ta mako-mako, yayin da kwale-kwalen ɗauke da fasinjoji da kayayyaki ya kife.
Darakta Janar na Hukumar NEMA, Zubaida Umar, ta ce cikin gaggawa hukumar ta ƙaddamar da bincike bayan samun rahoton faruwar lamarin.
Ƙoƙarin ceto








