An zaɓi matasan Nijar 500 domin samun horo a kyauta don koyon sana’o’i a Aljeriya

Horon, wanda Shugaban Aljeriya Abdelmadjid Tebboune ya bayar da gurbinsa kyauta, zai ƙunshi fannoni 19 na sana’o’i, kuma zai ɗauki tsakanin kwanaki 20 zuwa 45, gwargwadon sana’ar da aka zaɓa.

Newstimehub

Newstimehub

27 Sep, 2026

956a0df4 3c4e 4422 9ff2 e692c1de05eb 1790507304978

Nijar ta zaɓi matasa 500 domin tafiya ƙasar Aljeriya don su samu horo a kyauta don koyon sana’o’i, a wani ɓangare na ƙara ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin ƙasashen biyu.

Ministar Ayyuka, Ƙwadago da Samar da Ayyukan Yi ta Nijar, Aïssata Abdoulaye Tondi, ce ta jagoranci wani taron wayar da kan matasan a Yamai a ranar Asabar, 26 ga Satumba, gabanin tafiyarsu.

Horon, wanda Shugaban Aljeriya Abdelmadjid Tebboune ya bayar da gurbinsa kyauta, zai ƙunshi fannoni 19 na sana’o’i, kuma zai ɗauki tsakanin kwanaki 20 zuwa 45, gwargwadon sana’ar da aka zaɓa.

Tondi ta buƙaci matasan Nijar da su kasance masu ladabi, ɗaukar nauyi da kuma nuna muhimmanci a duk tsawon lokacin da za su yi a Aljeriya, tana mai jaddada cewa ɗabi’unsu za su shafi martabar ƙasarsu.

“Ku matasa 500 ne da aka zaɓa daga cikin dubban matasa domin wannan kyakkyawan horo a Jamhuriyar Aljeriya,” in ji ta, tana bayyana shirin a matsayin wata dama da aka samar a ƙarƙashin haɗin gwiwar Nijar da Aljeriya.

Ta kuma sanar da cewa za a bai wa waɗanda suka ci gajiyar shirin wani kundin bayanai da aka fassara zuwa Faransanci, Zarma da Hausa domin taimaka musu yayin zaman nasu.

Daraktan Ƙwadago da Samar da Ayyukan Yi, Seydou Marayé, ya ce an zaɓi matasan daga sassa daban-daban na ƙasar bisa la’akari da buƙatun kasuwar ƙwadago da Cibiyar Binciken Ayyukan Yi ta Ƙasa ta gano.

Fannonin sana’o’in 19 sun haɗa da aikin lantarki, gine-gine, aikin famfo da walda. Shirin zai kuma samar da tallafi domin taimaka wa mahalarta samun damar ayyuka yi bayan sun dawo Nijar da kuma amfani da ƙwarewar da suka samu.

An raba matasan zuwa rukuni biyu kuma ko wane rukuni tafiyarsa daban. Ana sa ran rukunin farko zai tashi daga Yamai da ƙarfe 11:50 na dare ranar 29 ga Satumba, yayin da rukuni na biyu zai tashi da ƙarfe 10:25 na safe ranar 30 ga Satumba.

Shirin na da nufin ƙara ƙarfafa haɗin gwiwar Nijar da Aljeriya a fannin koyar da sana’o’i da bunƙasa ƙwarewar matasa.