Fitaccen mawakin Ghana, Shatta Wale, wanda aka haifa da sunan Charles Nii Armah Mensah, an kama shi a Accra a wani bincike da ake yi a Amurka dangane da sayen motar Lamborghini.
A cewar Hukumar Yaki da Laifuka na Tattalin Arziki da Tsare-Tsare ta Ghana (EOCO), an yi wa Shatta Wale tambayoyi a ranar Laraba dangane da Lamborghini Urus ta shekarar 2019 da hukumomin Amurka ke zargin an saye ta ne da kudaden da aka samu daga wata damfara ta dala miliyan $4 da aka yi a Amurka.
Daruruwan masoya sun taru a wajen ofishin EOCO a Accra a ranar Alhamis, suna cewa za su kwana a wajen har sai an saki mawakin bayan an tsare shi sannan an shafe sa’o’i ana masa tambayoyi.
Binciken yana daga cikin wani babban bincike na damfara da ake yi a Amurka wanda ya shafi wani dan Ghana, Nana Kwabena Amuah, wanda yanzu haka yake zaman gidan yari a Amurka, in ji hukumar.
Hukumar EOCO ta bayyana cewa motar Lamborghini, wadda aka kwace tun farkon shekarar nan a Ghana, tana karkashin wata doka daga Kotun Gundumar Amurka ta Gabashin Kentucky, wadda ta ba da izini ga gwamnatin Amurka ta karbe motar a Ghana a matsayin diyya.
Mawakin ya isa ofishin EOCO a ranar Laraba da rana, inda ya jira lauyansa kafin a fara tambayoyi da suka dauki tsawon lokaci har zuwa yamma, kamar yadda sanarwar ta bayyana.