Amurka ta sanar da sabon tsarin biza ga ‘yan Nijeriya, inda ake bukatar duk masu neman biza su bayyana sunayen da suke amfani da su a shafukan sada zumunta na tsawon shekara biyar domin bincike a kansu.
‘‘Rashin bayar da bayanan kafafen sada zumunta na iya haifar da kin amincewa da bayar da biza da kuma rashin cancanta don samun biza a nan gaba,’’ in ji Ofishin Jakadancin Amurka a Nijeriya a cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa X a ranar Litinin.
Ya ƙara da cewa masu neman bizar ‘‘ana bukatar su lissafa duk sunayen da suke amfani da su a shafukansu na sada zumunta da suka yi amfani da su cikin shekaru 5 da suka gabata a fom ɗin neman biza na DS-160.’’
Gwamnatin Nijeriya har yanzu ba ta mayar da martani kan wannan sabon tsarin bizar na Amurka ba.
Wannan umarnin ya zo ne a yayin da Amurka ke ƙara tsaurara dokokin biza da kuma ƙaƙaba takunkumin tafiya ƙasashe daban-daban na duniya, musamman ƙasashen Afirka.
A watan Yuli, Nijeriya ta buƙaci gwamnatin Trump ta sake duba wata doka da ta taƙaita wa’adin biza na wucin gadi ga ‘yan Nijeriya zuwa watanni uku kacal. Wannan umarni ya kuma shafi Kamaru da Habasha.