Akalla mutane 14 sun rasa rayukansu sakamakon ruwan sama mai karfi da ambaliyar ruwa a arewaci da kudu maso gabashin Sudan, kamar yadda kafafen yada labarai na cikin gida suka bayyana a ranar Laraba.
Shaidu sun ce ruwan sama mai ƙarfi da ambaliyar ruwa sun lalata garuruwa da ƙauyuka da dama a Jihar River Nile, wanda ya haifar da katsewar wutar lantarki da kuma rushewar gine-gine da dama, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na jihar, SUNA, ya ruwaito.
Mutane shida sun rasu lokacin da gidaje suka rushe sakamakon ruwan sama mai ƙarfi a arewacin Jihar River Nile.
Wata uwa da ‘ya’yanta uku sun mutu a Jihar Sennar da ke kudancin Sudan bayan ɗakin gidansu ya rushe sakamakon ruwan sama mai karfi.
Mutane sun rasa matsuguni