Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Nijeriya (NEMA) ta ce aƙalla mutane 165 ne suka rasu, 82 suka ɓace sakamakon ambaliya a bana,
NEMA ta bayyana haka ne a ranar juma’a a wata ƙididdiga da ta fitar. Hukumar ta ce ambaliyar ta bana ta shafi aƙalla mutum 119,791 a bana.
Hukumar ta kuma bayyana cewa mutane 138 sun samu raunuka iri-iri, 43,936 sun rasa matsugunansu, gidaje 8,594 da gonaki 8,278 ne ambaliya ta shafa a cikin ƙananan hukumomi 43 da ke jihohi 19.
A cewar hukumar, yara da mata ne wannan bala’in ya fi shafa.
Ta ce, “Yara 53,314, mata 36,573, maza 24,600, tsofaffi 5,304 da kuma mutane 1,863 masu nakasa ne ambaliya ta shafa a bana.”
Jihohin da suka fi yawan waɗanda ambaliya ta shafa sun haɗa da Imo, Rivers, Abia, Borno da Kaduna.
A halin yanzu, jihohi 19 da ambaliya ta shafa sun haɗa da: Abia, FCT, Adamawa, Akwa Ibom, Anambra, Bayelsa, Borno, Edo, Gombe, Imo, Jigawa, Kaduna, Kano, Kogi, Kwara, Neja, Ondo, Rivers da Sakkwato.