Aƙalla mutane 30 ne suka rasa rayukansu bayan ambaliya mai tsanani ta afku a yankin Gamo na kudancin Habasha, sakamakon ruwan sama mai ƙarfi da aka shafe kwanaki ana samu. Hukumomi sun ce mafi yawan waɗanda suka mutu sun fito ne daga yankunan Degama, inda koguna suka cika suka kuma mamaye gidaje da sauran muhimman gine-gine.
Ruwan saman ya haddasa mummunar lalacewa ga gidaje da hanyoyin sadarwa, tare da jefa al’ummomi cikin mawuyacin hali. Mahukunta na ci gaba da tantance girman barnar da ambaliyar ta yi, yayin da ake ƙoƙarin taimakawa mutanen da bala’in ya shafa.
Lamarin ya zo ne a daidai lokacin da yankin Gabashin Afirka ke fama da matsanancin yanayi. A makwabciyar Kenya ma an samu mutuwar mutane da dama bayan ruwan sama mai ƙarfi ya haddasa ambaliya a Nairobi da wasu yankuna.
Masana sun yi gargadin cewa irin waɗannan manyan ruwan sama suna ƙara yawaita a yankin, inda bincike ya nuna ana fuskantar sauye-sauyen yanayi kamar ambaliya mai tsanani da kuma fari mai tsawo a cikin shekaru ashirin da suka gabata.














