Ambaliya ta halaka aƙalla mutum 47 da kuma raba dubbai da gidajensu a Nijar

Dubban mutane ne ambaliya ta raba da gidajensu tare da kashe dabbobi, in ji hukumomin ƙasar.

Newstimehub

Newstimehub

21 Aug, 2025

d053cdb89105d27ea118d55566e1ad15f124e5b307c31d26ddf8c6789432b690

Ambaliya ta kashe aƙalla mutum 47 tare da raba fiye da mutum 56,000 da gidajensu a Jamhuriyar Nijar, in ji hukumomin ƙasar a ranar Laraba.

Ambaliyar ta shafi gidaje 7,754 a cikin unguwanni da ƙauyuka 339 , in ji hukumar tsaron fararen hular ƙasar.

“Wasu mutum 30 sun mutu bayan gidajensu sun rushe yayin da mutum 17 suka nutse a ruwa.

“Kazalika ambaliyar ta raunata mutum 70 ta kuma haddasa mutuwar dabbobi 257,” in ji hukumar.

Kwamiti na ƙasa da aka ɗora wa alhakin hana ambliya ya ce ya fara raba tallafin abinci ga iyalai 3,776.