Jami’an tsaro a Somaliya sun kashe ‘yan ta’addan Al Shabab fiye da 50

Jami’an tsaron sun ce sun halaka ‘yan ta’addan ne a wani samame na musamman da suka kai garin Bariire a yunƙurinsu na ƙwato garin
4 Aug, 2025
Kwalara ta kashe mutum 80, mutum 2,100 sun kamu da ita a yankin Darfur na Sudan

Yara fiye da 640,000 na fuskantar barazanar tashin hankali da yunwa da kwalara a Arewacin Darfur, kamar yadda hukumar MDD ta bayyana a gargaɗinta
4 Aug, 2025
Ghana ta bayar da tallafin tan 40 na kayan agaji ga Falasdinu

Tallafin, wanda ya haɗa da kayayyakin da aka sarrafa da koko da wanda aka samar a Ghana, an miƙa su ga jakadan Falasdinu a Ghana, Abdul Fattah Ahmed Khalil al-Sattari, wanda ya bayyana godiya mai yawa.
3 Aug, 2025
Gidajen burodi a Nijar za su tafi yajin aikin gargaɗi na kwana biyu

Gidajen burodi da sauran masu sarrafa fulawa a Nijar za su tafi yajin aikin ne sakamakon wata sabuwar doka wadda ta tilasta musu amfani da fulawa nau’in T55 da T65 da ba a iya samu a ƙasar cikin sauƙi
3 Aug, 2025

Burkina Faso ta dakatar da wani gidan rediyo bayan ya kira gwamnatin ƙasar ‘ta mulkin soji’

‘Yan bindiga sun kashe mutum uku da sace matan aure a Nijar

Gwamnatin Ghana za ta fara cin tarar direbobin da ke lodi fiye da ƙima Cedi 50,000

MDD ta ce yara 80,000 na cikin haɗarin kamuwa da cutar kwalara a Yammaci da Tsakiyar Afirka

An samu mace-macen farko da ke da alaƙa da Mpox a Ghana yayin da cutar ke yaɗuwa cikin sauri
29 Jul, 2025
Nijar da Rasha sun rattaba hannu kan yarjejeniyar makamashin nukiliya da haƙar yuraniyom
Kamfanin dillancin labaran Nijar (ANP) ya ruwaito cewa ƙasashen biyu sun sanya hannu a yarjejeniyar ce ranar Litinin yayin ganawar shugaban Nijar, Janar Abdourahamane Tiani, da wata tawagar Rasha ƙarƙashin jagorancin ministan makamashi, Mista Sergei

27 Jul, 2025
Amurka ta dakatar da ayyukan bayar da biza a ofishin jakadancinta na Nijar
Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta ce wannan matakin da ta ɗauka kan Nijar zai ci gaba da kasancewa har sai ta warware matsalolin da take da su da ƙasar.

26 Jul, 2025
Senegal ta haramta amfani da babura a kusa da iyakarta da Mali
Dokar hana amfani da baburan wadda za ta rinƙa aiki daga tsakar dare zuwa wayewar gari ta shafi yankin Bakel na Senegal, wanda ke da tsayin kilomita 230 a kan iyaka da Mali.

26 Jul, 2025
Mutum fiye da 1.3M sun koma gida Sudan, MDD na buƙatar ƙarin tallafi
Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci yi gaggawar ƙara tallafin kuɗi domin farfaɗo da yankunan da rikici ya ɗaiɗaita, yayin da ‘yan Sudan da rikici ya raba da muhallansu suka fara komawa gida.

2 Jun, 2025
‘Yan ta’adda sun ƙwace sansanin soji a Mali, sun ‘kashe sojoji fiye da 30’
Tun farkon watan Mayu, an ruwaito cewa fiye da sojoji 400 sun rasa rayukansu a hannun ‘yan bindiga a sansanoni da garuruwa a Mali, Nijar, da Burkina Faso.

1 Jun, 2025
Shugaba Tiani na Nijar ya ce har yanzu Faransa ba ta daina yi musu bi-ta-da-ƙulli ba
Shugaban Tiani ya zargi Faransa da hannu a kusan duka rikice-rikicen da suka faru a ƙasashen duniya waɗanda suka haɗa da Pakistan da Afghanistan da Iraƙi da Syria da Libiya.

30 May, 2025
Mutum fiye da 1,300 sun kamu da cutar kwalara a cikin kwana guda a Sudan
Ko a ranar Laraba sai da ma’aikatar lafiya ta Jihar Khartoum ta sanar da samun mutum 942 da suka kamu da cutar kwalara da kuma mutuwar mutum 25 a ranar Talata, yayin da a ranar Litinin aka samu mutum 1,177 da suka kamu da cutar da mutuwar mutum 25.

29 May, 2025
Sidi Ould Tah ya zama sabon Shugaban Bankin Raya Ƙasashen Afirka AfDB
Masanin tattalin arzikin mai shekaru 60 da haihuwa shi ne na ƙarshe da ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takara kuma ya gudanar da yakin neman zaɓe inda ya bayyana shekaru 10 da ya yi a matsayin Shugaban Bankin Larabawa na Bunkasa Tattalin Arzikin Afirk

29 May, 2025
An yanke wa wata mata ‘yar Afirka ta Kudu hukuncin daurin rai da rai saboda sayar da ‘yarta
An yanke wa Racquel Smith da wasu mutane biyu da aka gurfanar da su tare hukuncin daurin rai da rai saboda safarar bil’adama, da kuma hukuncin shekara 10 saboda satar mutane

28 May, 2025
ECOWAS ‘tana da ƙwarin gwiwar’ cewa Burkina Faso, Mali da Nijar za su koma cikin kungiyar
Ƙungiyar ECOWAS ta Yammacin Afirka ta ce, tana da ƙarin gwiwar cewa Burkina Faso da Mali da Nijar za su koma cikinta bayan ficewarsu a Janairun 2025.



