Ƙungiyar RSF ta Sudan ta kashe fararen hula 18 a yammacin Khartoum

Ƙungiyar RSF wadda ke rikici da sojojin Sudan ta kashe mutanen ne a wani hari da suka kai kan ƙauyuka biyu da ke yammacin Khartoum.
10 Aug, 2025
Gwamnatin Nijar ta ƙwace mahaƙar zinari daga kamfanin Australia

Gwamnatocin mulkin soji na Jamhuriyar Nijar da maƙotansu Burkina Faso da Mali sun matsa lamba kan kamfanonin haƙar ma’adanai na ƙasashen waje a shekarun baya bayan na, inda Nijar ta ƙwace kamfanin haƙar yuraniyom na Faransa, Orano a watan Yuni.
9 Aug, 2025
Rundunar Sojin Ghana za ta yi cikakken bincike kan hatsarin helikwafta – Mahama

Shugaban ƙasar ya ce za a yi wa waɗanda suka mutu a hatsarin jana’iza ta ƙasa.
8 Aug, 2025
Ana makokin kwana uku a Ghana sakamakon rasuwar wasu ministoci a hatsarin helikwafta

Ranar Laraba ne dai wani jirgin helikwafta na sojin ƙasar ya yi hatsari, lamarin ya yi sanadin rasuwar ministoci biyu da wasu jami’an ƙasar Ghana.
7 Aug, 2025

Ministan Tsaro da na Muhalli da Kimiyya na Ghana sun rasu a hatsarin helikwafta

Shoprite na shirin ficewa daga Ghana da Malawi

Gwamnatin Ghana ta ƙara farashin da manoma za su sayar da cocoa

Rwanda ta amince za ta karɓi baƙin haure 250 da aka kora daga Amurka

Nijar za ta sayo na’urori tare da gina sashen gwajin ciwon daji kan dala miliyan biyu
4 Aug, 2025
Ghana ta bai wa kamfanin MultiChoice wa’adi ya rage kuɗin kallo ga kwastamomi ko a dakatar da shi
Kamfanin MultiChoice wanda ya mallaki DSTV da GOTV, ya fuskanci matsaloli na shari’a a shekarun da suka gabata a ƙasashe da dama dangane da ƙarin farashi da saɓani kan haraji.

4 Aug, 2025
Jami’an tsaro a Somaliya sun kashe ‘yan ta’addan Al Shabab fiye da 50
Jami’an tsaron sun ce sun halaka ‘yan ta’addan ne a wani samame na musamman da suka kai garin Bariire a yunƙurinsu na ƙwato garin

4 Aug, 2025
Kwalara ta kashe mutum 80, mutum 2,100 sun kamu da ita a yankin Darfur na Sudan
Yara fiye da 640,000 na fuskantar barazanar tashin hankali da yunwa da kwalara a Arewacin Darfur, kamar yadda hukumar MDD ta bayyana a gargaɗinta

3 Aug, 2025
Ghana ta bayar da tallafin tan 40 na kayan agaji ga Falasdinu
Tallafin, wanda ya haɗa da kayayyakin da aka sarrafa da koko da wanda aka samar a Ghana, an miƙa su ga jakadan Falasdinu a Ghana, Abdul Fattah Ahmed Khalil al-Sattari, wanda ya bayyana godiya mai yawa.

3 Aug, 2025
Gidajen burodi a Nijar za su tafi yajin aikin gargaɗi na kwana biyu
Gidajen burodi da sauran masu sarrafa fulawa a Nijar za su tafi yajin aikin ne sakamakon wata sabuwar doka wadda ta tilasta musu amfani da fulawa nau’in T55 da T65 da ba a iya samu a ƙasar cikin sauƙi

3 Aug, 2025
Burkina Faso ta dakatar da wani gidan rediyo bayan ya kira gwamnatin ƙasar ‘ta mulkin soji’
Hukumar kula da kafafen yada labarai ta kasar (CSC) ce ta sanar da hakan a wata sanarwa da ta fitar a ranar Asabar, inda ta ce gidan rediyon ba zai iya watsa shirye-shirye ko wallafa wani abu a kafafensa na sada zumunta ba har sai bayan wata uku.

1 Aug, 2025
‘Yan bindiga sun kashe mutum uku da sace matan aure a Nijar
‘Yan bindigar sun kai hare-hare biyu a yankin Maradi na Jamhuriyar Nijar inda suka kashe mutum uku tare da sace matan aure da ‘yan mata.

1 Aug, 2025
Gwamnatin Ghana za ta fara cin tarar direbobin da ke lodi fiye da ƙima Cedi 50,000
Gwamnatin Ghana ta ce hanyoyin ƙasar da dama sun lalace sakamakon lodi fiye da ƙima da ake yi wa motoci wanda hakan ya sa za a ƙara yawan tarar da ake cin direbobin da suka saɓa doka daga Cedi 5,000 zuwa Cedi 50,000.

31 Jul, 2025
MDD ta ce yara 80,000 na cikin haɗarin kamuwa da cutar kwalara a Yammaci da Tsakiyar Afirka
Ɓarkewar annobar kwalara a Jamhuriyar Dimokradiyyar Kongo da Nijeriya ya jawo fargabar cewa za a iya samun yaɗuwar cutar a tsakanin ƙasashe maƙwabta, in ji Hukumar Majalisar Dinkin Duniya

29 Jul, 2025
An samu mace-macen farko da ke da alaƙa da Mpox a Ghana yayin da cutar ke yaɗuwa cikin sauri
An tabbatar da ƙarin mutane 23 sun kamu da cutar a makon jiya, wanda ya kawo adadin waɗanda suka kamu da cutar zuwa 257 tun lokacin da aka fara gano ta a Ghana a watan Yunin 2022.


