An tsare mawaƙin Ghana Shatta Wale kan zargin wata damfara da aka yi a Amurka ta sayen motar alfarma

Ana zargin Shatta Wale da sayan wata mota ƙirar Lamborghini wadda ake zargin an saye ta ne da kudaden da aka samu daga wata damfara ta dala miliyan $4 da aka yi a Amurka.
22 Aug, 2025
Ambaliya ta halaka aƙalla mutum 47 da kuma raba dubbai da gidajensu a Nijar

Dubban mutane ne ambaliya ta raba da gidajensu tare da kashe dabbobi, in ji hukumomin ƙasar.
21 Aug, 2025
An kama ɗan Muhammad Yusuf, tsohon shugaban Boko Haram a Chadi – Rahotanni

Rahotanni daga Chadi na cewa an cafke wani ƙaramin ɗan cikin wanda ya kafa ƙungiyar Boko Haram, wanda ke jagorantar wani gungun ‘yan ta’adda.
19 Aug, 2025
Shugaban Ghana Mahama ya yi wa fursunoni kusan 1000 afuwa

Sauran sun haɗa da mutum 33 da suke rashin lafiya da mutum 33 da shekaraunsu ya ɗara 70 da mata masu shayarwa biyu da kuma mutum biyu da suka kai ƙara.
19 Aug, 2025

Gwamnatin Nijar ta ƙwato fiye da FCFA biliyan 63.8 a yaƙi da cin hanci

Dakarun RSF na Sudan sun kashe gomman mutane a wani sansanin ‘yan gudun hijira a Darfur

Rasha ta yi alƙawarin bai wa Mali da Nijar da Burkina Faso tallafin soji

Ambaliyar ruwa ta kashe mutum 23 a Jamruriyar Nijar

Ghana ta rufe gidajen rediyo tara kan saɓa ƙa’idojin watsa labarai
14 Aug, 2025
Kwamitin Sulhu na MDD ya yi watsi da yunƙurin RSF na kafa sabuwar gwamnati a Sudan
Majalisar ta nemi a tsagaita wuta cikin gaggawa a El Fasher, tana mai cewa wani yunƙuri da dakarun RSF ke yi na kafa sabuwar gwamnati zai ƙara rura wutar rikici a Sudan.

12 Aug, 2025
Ghana ta umarci shugabannin addini su dinga miƙa mata ‘saƙonnin ikirarin wahayi’ don tantancewa
Umarnin gwamnatin na zuwa ne bayan hatsarin helikwafta ya kashe jami’ai takwas, inda ake iƙirarin cewa wasu limaman addinin Kirista sun bayyana cewa lamarin zai auku kafin hatsarin.

11 Aug, 2025
Ma’aikatar Shari’ar Nijar ta yi bayani game da rushe ƙungiyoyin ƙwadago
Kamfanin dillancin labaran Nijar(ANP) ya ambato wata sanarwar da ministan shari’ar ƙasar, Alio Daouda, ya fitar tana cewa an yi ammanar cewa ƙungiyoyin ƙwadagon huɗu ba sa aiki domin inganta aikin ɓangaren shari’a domin kare muradun al’umma.

10 Aug, 2025
An yanke wa tsohon Firaministan Chadi Succes Masra hukuncin ɗaurin shekara 20 a gidan yari
Wata kotu ta musamman a babban birnin Chadi, N’djamena, ta same shi da laifin furta kalaman ƙiyayya da nuna ƙiyayya ga baƙi da kuma tunzura jama’a domin aikata kisan-kiyashi.

10 Aug, 2025
Ƙungiyar RSF ta Sudan ta kashe fararen hula 18 a yammacin Khartoum
Ƙungiyar RSF wadda ke rikici da sojojin Sudan ta kashe mutanen ne a wani hari da suka kai kan ƙauyuka biyu da ke yammacin Khartoum.

9 Aug, 2025
Gwamnatin Nijar ta ƙwace mahaƙar zinari daga kamfanin Australia
Gwamnatocin mulkin soji na Jamhuriyar Nijar da maƙotansu Burkina Faso da Mali sun matsa lamba kan kamfanonin haƙar ma’adanai na ƙasashen waje a shekarun baya bayan na, inda Nijar ta ƙwace kamfanin haƙar yuraniyom na Faransa, Orano a watan Yuni.

8 Aug, 2025
Rundunar Sojin Ghana za ta yi cikakken bincike kan hatsarin helikwafta – Mahama
Shugaban ƙasar ya ce za a yi wa waɗanda suka mutu a hatsarin jana’iza ta ƙasa.

7 Aug, 2025
Ana makokin kwana uku a Ghana sakamakon rasuwar wasu ministoci a hatsarin helikwafta
Ranar Laraba ne dai wani jirgin helikwafta na sojin ƙasar ya yi hatsari, lamarin ya yi sanadin rasuwar ministoci biyu da wasu jami’an ƙasar Ghana.

6 Aug, 2025
Ministan Tsaro da na Muhalli da Kimiyya na Ghana sun rasu a hatsarin helikwafta
Babban hafsan hafsoshin kasar Ghana Julius Debrah ya sanar a ranar Laraba cewa helikwaftan ya yi hatsarin ne yayin da yake kan hanyarsa ta zuwa Obuasi da ke kudancin Ghana daga Accra babban birnin kasar.

6 Aug, 2025
Shoprite na shirin ficewa daga Ghana da Malawi
A ƙasar Ghana, an taya kantunan kamfanin bakwai da kuma ɗakin ajiya ɗaya a watan Yuni. Yiwuwar cinikin ya faɗa na da ƙarfi sosai, in ji Shoprite.


