Hukumar EFCC mai yaƙi da masu yi wa tattalin arzikin Nijeriya ta’annati ta yi shelar neman Abdullahi Bashir Haske, surukin tsohon mataimakin shugaban ƙasar Atiku Abubakar, ruwa-a-jallo.
Wata sanarwar da EFCC ta wallafa a shafukanta na sada zumunta ranar Alhamis da maraice ta ce hukumar tana neman mutumin ne bisa zargin halatta kuɗin haram da haɗa baki domin aikata laifuka.
Sanarwar da shugaban fannin hulɗa da jama’a na hukumar, Dele Oyewale, ya sanya wa hannu, ta ce Abdullahi Bashir Haske mai shekara 38, an san shi ne da zama a gida mai lamba ta 6 a kan titin Mosley a unguwar Ikoyi da ke birnin Legas.