Gwamnatin Katsina ta dakatar da Sarkin Daura kan zargin cin zarafin Baturiya

Gwamnatin ta kuma kafa wani kwamiti da zai gudanar da bincike kan zargin, wanda ya yaɗu a shafukan sada zumunta.

Newstimehub

Newstimehub

24 Nov, 2026

a907a4bb decd 4965 8700 3a27ab610a8b 1795541403704

Gwamnatin Jihar Katsina ta dakatar da dukkan ayyukan hukuma da tafiye-tafiyen Sarkin Daura, Alhaji Umar Farouk Umar, biyo bayan zargin cin zarafin wata baƙuwar yawon buɗe ido da ake yi masa.

Gwamnatin ta kuma kafa wani kwamiti da zai gudanar da bincike kan zargin, wanda ya yaɗu a shafukan sada zumunta.

Kwamishinan Yaɗa Labarai da Al’adu na jihar, Bala Salisu Zango, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a yammacin Talata.

Sanarwar ta ce Gwamna Dikko Umaru Radda ne ya bayar da umarnin kafa kwamitin domin gudanar da bincike kan lamarin tare da ba gwamnati shawarwarin matakin da ya kamata ta ɗauka.

Gwamnatin ta ce tana matuƙar damuwa da zargin, tare da tabbatar da cewa za ta yi adalci, kuma za ta aiwatar da sakamakon binciken kwamitin da shawarwarinsa.

Ta kuma yi kira ga al’ummar jihar da su kwantar da hankalinsu, su kiyaye doka tare da ci gaba da harkokinsu na yau da kullum.