Rundunar ‘yansandan jihar Borno da ke arewa maso gabashin Nijeriya ta kama mutum 103 da ake zargi da aikata laifuka da suka haɗa da ta’ammali da miyagun ƙwayoyi da dabanci da sauran laifuka a cikin wani aikin da ta shafe mako ɗaya tana yi a birnin Maiduguri da kewaye.
Aikin, wanda ya kuma yi silar ƙwace wasu miyagun ƙwayoyi da makamai masu hatsari, an yi shi ne tsakanin ranar 29 ga watan Oktoba da ranar 2 ga watan Nuwamba na shekarar 2026.
A wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, ASP Nahum Daso, ya sanya wa hannu kuma aka wallafa shafin X na rundunar ranar Talata, rundunar ta bayyana aikin a matsayin nasara a ƙoƙarinta na kawar da masu aikata laifuka daga birnin.
Ya ce aikin ya haɗa da tawagar ‘yansanda da jami’ai daga sauran hukumomin tsaro, waɗanda suka kai samame da sintiri a wasu wurare da aka fi sani da aikata laifuka da lamura na rashin tsaro.
Wuraren da lamarin ya shafa sun haɗa da Gwange da Santiago da Texaco da Ajari da Gadan Zare da Budum da Shehuri da Bulabulin da Abbaganaram da Baga Road da Gidan Dambe da UNIMAID 202 Housing Estate da Mairi Kuwait da Bakari da Zanneri da Polo da Giwa Barrack Area da Kwanan Yobe da Jiddari da Kaleri da Damboa Road da Circular da kuma Moduganari da sauransu.
Daso ya ce an kama waɗanda ake zargin ne bisa laifuka da suka haɗa da damun jama’a da ta’ammali da kuma sayar da miyagun ƙwayoyi da kuma riƙe makamai masu hatsari.
Mai magana da yawun ‘yansandan ya ƙara da cewa an ƙwace nau’o’i na miyagun ƙwayoyi har 11.















