Kwalara ta kashe wasu fursunoni a gidan gyaran hali na Kurmawa da ke Kano

Hukumomi sun ce an gano mutum na farko da ya kamu da cutar a ranar 17 ga Satumba, lokacin da wani fursuna ya nuna alamun amai da gudawa, kuma nan take aka kwantar da shi aka ba shi magani a cibiyar kula da lafiya ta gidan gyaran halin.

Newstimehub

Newstimehub

27 Sep, 2026

86bd7328 1d56 4fcd 8178 255498d215a2 1790493374495

Fursunoni biyu sun mutu sakamakon ɓarkewar cutar kwalara a Gidan Gyaran Hali na Kurmawa mai matsakaicin tsaro da ke Jihar Kano.

Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali ta Nijeriya (NCoS) ce ta tabbatar da mutuwar a cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Asabar.

A cewar kakakin hukumar, CSC. JN Osuji, gwaje-gwajen ɗakin bincike da aka gudanar a ranar 23 ga Satumba sun tabbatar da ɓarkewar cutar.

Ya ce an fara gano ɓarkewar cutar ne a ranar 17 ga Satumba, bayan wani fursuna ya fara nuna alamomin cutar da suka haɗa da amai da gudawa.

Ya ce nan take aka kwantar da fursunan kuma aka ba shi magani a cibiyar kula da lafiya ta gidan yarin, yayin da aka fara aiwatar da matakan gaggawa na kiwon lafiya washegari da safe.

“Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali ta Nijeriya ta tabbatar da cewa an shawo kan ɓarkewar cutar kwalara a Gidan Gyaran Hali na Kurmawa mai matsakaicin tsaro da ke Kano.

“Ƙungiyar likitocin hukumar da hukumomin kula da lafiyar jama’a na Jihar Kano sun tabbatar da ɓarkewar cutar a ranar 23 ga Satumba,” in ji sanarwar hukumar.

Hukumomin sun ce an gano mutum na farko da ya kamu da cutar a ranar 17 ga Satumba, lokacin da wani fursuna ya nuna alamun amai da gudawa, kuma nan take aka kwantar da shi aka ba shi magani a cibiyar kula da lafiya ta gidan gyaran halin.

 “Mutane biyu sun mutu — ɗaya a gidan gyaran hali, ɗayan kuma a Asibitin Kula da Masu Cututtuka Masu Yaɗuwa na Jihar Kano.

“Babban Kwanturola-Janar na Gidan Gyaran Hali, Sylvester Nwakuche, ya bayar da umarnin ci gaba da ba da kulawar lafiya, sanya ido da kuma ɗaukar matakan kariya tare da haɗin gwiwar Gwamnatin Jihar Kano.

“Hukumar ta ce ba a sake samun ƙarin mutuwa ba tun bayan tabbatar da ɓarkewar cutar.”

Hukumar NCoS ta ce matakan da ta ɗauka sun taimaka wajen shawo kan ɓarkewar cutar, inda ta ƙara da cewa ba a sake samun wasu mace-mace ba tun bayan gano cutar.

Ta ce an ƙara ɗaukar wasu matakan kariya tare da haɗin gwiwar Gwamnatin Jihar Kano domin hana sake barkewar cutar.