Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya ce ya kamata a bar Musulmai su yi cuɗanya a cikin al’ummomin da suke zaune ba tare da tsangwamarsu ko kuma neman su yi watsi da harshensu da al’adunsu ko asalinsu ba.
“Abin takaici, akwai matsaloli a sassa da dama na duniya, musamman a Turai inda ba a son cuɗanya da Musulmai ake kuma nuna musu wariya. Muna cewa ‘e’ ga haɗin kai da ‘a’a’ ga kowane yanayi na nuna wariya,” in ji Erdogan.
Shugaban ya bayyana hakan ne a jawabin da ya gabatar a wani taro da Kwamitin Gudanarwa na Ƙasa tsakanin Turkiyya da Amurka (TASC) da kuma ƙungiyar ‘Yan Democrat ta Duniya (UID) da Ƙungiyar Masana’antu da ‘Yan Kasuwa Masu Zaman Kansu (MUSIAD) da kuma Majalisar Ƙungiyoyin Musulmai ta Amurka (USCMO) suka shirya a Gotham Hall da ke New York.
Ya ce mambobin al’ummar Turkiyya za su iya ƙarfafa matsayinsu a harkokin siyasa, da tattalin arziki, da zamantakewa da al’adu yayin da suke riƙe da harshensu, al’adunsu da alaƙarsu da ƙasarsu.
“Koyon harshensu da al’adunsu da kuma kiyaye alaƙar da ke tsakaninsu da ƙasarsu ba cikas ba ne ga haɗin kai,” in ji Erdogan.
Ya yi kira da a ƙara wa Turkawa ‘yan Amurkan damar wakilci a siyasa da kasuwanci da ilimi da al’adu da fasaha, yana mai cewa,ya kamata a haɓaka nasarorin da wani ya samu zuwa cibiyoyi masu ƙarfi da kuma tsare-tsare masu ɗorewa waɗanda za a iya ci gaba da moriyarsu a gaba.
Erdogan ya ce al’ummomi masu ƙarfi da haɗin kai za su iya taimakawa wajen yaƙi da ƙiyayya da tsangwama da kuma nuna wariya ga al’ummar Musulmai.
Ya buƙaci a dama a zaɓukan tsakiyar wa’adi na Amurka
Erdogan ya kuma yi tsokaci kan zaɓen tsakiyar wa’adi na Amurka mai zuwa, yana mai kira ga ‘yan ƙasa da su yi amfani da haƙƙinsu na dimokuraɗiyya da kuma muryoyinsu.
“Ina kira ga dukkan ‘yan ƙasarmu da su yi amfani da haƙƙinsu na dimokuraɗiyya a zaɓen tsakiyar wa’adi mai zuwa. Yana da matuƙar muhimmanci ku nuna muraɗunku a akwatin zaɓe a matakin mafi girma,” in ji shi.
Ya yi kira ga membobin al’umma da su ci gaba da ayyukansu a Amurka tare kuma cikin haɗin kai, da tsausayin juna da kuma ‘yan uwantaka.
Kazalika Shugaba Erdogan ya yaba wa ayyukan TASC da sauran ƙungiyoyin fararen hula, inda ya ce Turkiyya za ta ci gaba da tallafawa ‘yan ƙasarsa da al’ummomin Turkiyya da ke zama Amurka.
“Ina so ku sani cewa Turkiyya da mu baki ɗaya, za mu ci gaba da goyon bayanku a koyaushe kuma a shirye muke mu samar muku da kowane irin tallafi,” in ji shi.















