Kun san ƙasashen Afirka tara da suka kai zagayen sili-ɗaya-ƙwale a Gasar Kofin Duniya ta 2026?

Tunisiya ce ƙasa ɗaya tilo ta Afirka da aka fitar daga Gasar Kofin Duniya a matakin rukuni.

Newstimehub

Newstimehub

28 Jun, 2026

2026 06 15t214557z 707778134 rc2hular2m44 rtrmadp 3 soccer worldcup esp cpv fans praia

Tara daga ciki ƙasashe goma na Afirka da ke fafatawa a Gasar Kofin Dunita ta FIFA ta shekarar 2026 sun yi nasarar kai wa zagayen sili-ɗaya-ƙwale, inda Tunisiya ce ƙasa ɗaya tilo da aka fitar daga gasar a matakin rukuni.

Maroko da Afirka ta Kudu da Ivory Coast da Masar da Cape Verde da Senegal da Ghana da Aljeriya da kuma Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo duka sun yi nasarar zuwa zagayen ‘yan-32.

Tunisiya, ƙasar Afirka ɗaya tilo da aka fitar a matakin rukuni, ta gaza matsawa zuwa zagayen sili-ɗaya-ƙwale.

Sauran ƙasashen tara za su fafata a matakin ‘yan-32 a ayin da gasar ta shiga zagayen sili-ɗaya-ƙwale.

Brazil ce take kan gaba a Rukuni C, inda Maroko take biye mata. Mexico tana kan gaba a Rukunin A, inda Afirka ta Kudu take a mataki na biyu.

Jamus kuma ita ce ke kan gaba a Rukunin E inda ta zarta Ivory Coast da bambancin ƙwallaye.

Masar tana biye da Belgium wadda ke kan gaba a Rukunin G, yayin da Cape Verde ta bai wa kowa mamaki a wannan gasa, inda take biye da Sifaniya kuma ta zama ƙasa mafi ƙanƙantar jama’a da ta kai zagayen sili-ɗaya-ƙwale a gasar Kofin Duniya.

Senegal da Aljeriya su ne na uku a Rukunin I da J, inda suke biye da Faransa/Norway da Argentina/Austria.

Ghana ta kai zagayen sili-ɗaya-ƙwale daga Rukunin L, inda take biye da Ingila da Croatia, yayin da Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo ta zo ta uku a Rukunin K, inda take biye da Colombia da Portugal.