Mutane uku sun mutu bayan motar fasinja ta yi karo da giwa a gandun dajin Uganda

Motar tana ɗauke da ma’aikatan Hukumar Haraji ta Uganda.

Newstimehub

Newstimehub

26 May, 2026

1750246520538 qcrep9 5494b1820a70c81d3ea8c9802213989c5d44f4c89950f7fd9320a9de53f1d996

Wata motar fasinja ta kaɗe giwa a gandun dajin Uganda, abin da ya yi sanadin mutuwar mutane uku sannan wasu huɗu suka jikkata, in ji ‘yan sanda.

Wata sanarwa da ‘yansanda suka fitar a ranar Litinin tace, hatsari ya auku a ranar Lahadi a kan titin da aka shimfida a cikin Gandun Daji Murchison Falls na Ƙasa.

Motar na ɗauke da ma’aikatan Hukumar Haraji ta Uganda waɗanda suke tafiya daga wani birni a arewacin Uganda zuwa Kampala, babban birnin ƙasar.

Sanarwar ‘yan sandan ta ce, bayan kaɗe dabbar, direban “ya kasa sarrafa motar”. “Ana kira ga direbobi su yi taka-tsantsan matuƙa yayin tuki a cikin gandunan daji na ƙasa da yankunan da ake killace namun daji.”

Bidiyon da aka ɗauka a wurin ya nuna mutanen da ke cikin motar da ta lalace suna kukan neman agaji, yayin da giwar da ta ji rauni ke ƙoƙarin tashi daga cikin ciyayi da ke kusa. Ba a tabbatar ko giwar ta rayu ba.