Ƙungiyar Tarayyar Afirka ta sha alwashin goyon bayan Nijar bayan kai hari a filin jirgin saman Yamai

‘Wannan ɗanyen aiki wani ɓangare ne na ta’addanci da ƙungiyoyi masu tsattsauran ra’ayi suka yi da gangan domin tayar da hankalin fararen-hula da lalata ababen more rayuwa,’ in ji shugaban hukumar Tarayyar Afirka.

Newstimehub

Newstimehub

31 Jan, 2026

1764583280916 ss8f2e 59005d2608bfad75d3d5e0fd750de3e52c4afa34d7268455122ddb849faaced8

Shugaban Hukumar Tarayyar Afirka, Mahmoud Ali Youssouf, ya yi Allah wadai da harin da aka kai Filin Jirgin Saman Hamani Diori na birnin Yamai a Nijar, sannan ya jaddada goyon bayan hukumar ga gwamnatin Nijar.

Youssouf ya ce ya yi “matuƙar damuwa” bisa harin da ‘yanbindiga suka kai filin jirgin saman Yamai ranar Alhamis da daddare da kuma wanda suka kai ranar 18 ga watan Janairu a ƙauyen Bosiye da ke yammacin Nijar, inda suka kashe kimanin mutum 30.

“Wannan ɗanyen aiki wani ɓangare ne na ta’addanci da ƙungiyoyi masu tsattsauran ra’ayi suka yi da gangan domin tayar da hankalin fararen-hula da lalata ababen more rayuwa,” in ji shugaban hukumar Tarayyar Afirka.

Ya jinjina wa jami’an tsaron Nijar bisa yadda suka “gaggauta mayar da martani” wanda ya taimaka wajen daƙile harin.

Shugaban Hukumar Tarayyar Afirka ya jaddada goyon bayan ƙungiyar ga al’ummar Nijar sannan ya miƙa saƙon ta’aziyyarsa ga iyalan waɗanda lamarin ya shafa da kuma gwamnatin Jamhuriyar Nijar.

Kazalika Youssouf ya yaba wa gwamnatin Nijar kan yaƙin da take yi da ta’addanci, inda ya bayar da misali game da yadda dakarun ƙasar suke fafutukar kawar da ‘yanta’adda.