Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya fice daga Jam’iyyar NNPP

Gwamnan ya ce ya fice daga jam’iyyar ne sakamakon rikicin cikin gida da ya dabaibaye jam’iyyar ta NNPP.

Newstimehub

Newstimehub

23 Jan, 2026

6422614847862c1fa4c7f9a861a3ebdd95eb5c372babfd988ca7983d358e28e7

Gwamnan Jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya fice daga Jam’iyyar NNPP mai mulki a jihar.

Mai magana da yawunsa Sanusi Bature Dakin-Tofa ne ya sanar da ficewar gwamnan a ranar Juma’a.

Gwamnan ya ce ya fice daga jam’iyyar ne sakamakon rikicin cikin gida da ya dabaibaye jam’iyyar ta NNPP.

Sanarwar ta ce gwamnan ya aika da wasiƙa a hukumance ga ofishin NNPP da ke mazaɓar Diso-Chiranchi a Ƙaramar Hukumar Gwale inda ya sanar da batun ficewar tasa a ranar Juma’a, 23 ga Janairun 2026.

Hakazalika sanarwar ta ƙara da cewa gwamnan ya fice daga NNPP ɗin ne tare da ‘yan majalisar dokokin jiihar 21 da ‘yan majalisar tarayya takwas.

An dai shafe makonni ana raɗe-raɗin ficewar gwamnan daga jam’iyyar NNPP inda ake hasashen cewa zai koma Jam’iyyar APC mai mulki.

Ko a makon nan sai da gwamnan na Kano ya yi ganawar sirri da shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu, duk cewa fadar gwamnatin ta Kano ta ce tattaunawar ta mayar da hankali ne kan batun tsaro da kuma hanyoyin da za a bunƙasa jihar.