‘Yan jarida bakwai mambokin Kungiyar ‘Yan Jarida ta Kasa (NUJ) sun rasa rayukansu a hanyarsu ta dawowa daga ɗaurin auren abokin aikinsu a Ƙaramar Hukumar Kaltungo da ke jihar Gombe a arewacin Nijeriya.
Bayan halartar ɗaurin auren, tayar motar bas ɗin da suke ciki ta fashe a kan hanyarsu ta komawa gida a kusa da garin Kumo, Ƙaramar Hukumar Akko, inda motar ta ƙwace wa direban tare da nufar cikin daji.
Kwamandan Hukumar Kiyaye Hadurra ta Tarayya (FRSC) reshen Gombe, Samsan Kaura da Darakta Janar na Watsa Labaran Gidan Gwamnati, Ismaila Misilli, sun tabbatar da rasuwar mutanen bakwai, inda wasu huɗu kuma suka jikkta, kuma suna samun kulawa a asibiti.
Waɗanda suka rasa rayukansu sun haɗa da Zarah Umar, Manajar Labarai kuma Babbar Mataimakiya ta Musamman ga Gwamna a Ofishin matar Gwamna; Manu Haruna Kwami, Manajan Gudanarwa a NTA, da Musa Tabro, Manajan Labarai da ya yi ritaya.
Sauran sun haɗa da Aminu Adamu, Babban Direba; Adams Danladi na Star Times; Judith Kutus, Jami’in Yada Labarai a Hukumar Ilimin Bai Daya ta Jihar Gombe.
Tuni Gaamna Inuwa Yahaya ya mika sakon ta’aziyya ga iyalan wadanda suma mutu inda ya yi musu fatan samun rahma da sauki cikin gaggawa ga wadanda suka jikkata.
Gwamnan ta bakin Misilli ya ce “Wannan ibtila’i na da bakanta rai. Mun rasa abokan aiki, abokan kawo cigaba, kuma ma’aikata da suka sadaukar da kawunansu wajen hidimtawa al’umma.”
Ya kara da cewa zukatansu kuma na tare da wadanda suka jikkata, suna kuma yi musu fatan samun sauki cikin gaggawa.









