Akalla mutane 13 sun rasu sannan fiye da 20 sun ɓace a jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin Nijeriya bayan jirgin ruwan da suka hau don tsere wa harin wasu ‘yan bindiga ya kife a cikin kogi, kamar yadda mazauna yankin da jami’ai suka bayyana a ranar Asabar.
Zamfara na ɗaya daga cikin jihohin Nijeriya da ‘yan bindiga ke yawan kai hare-hare.
Maharan sun kai hari kan ƙauyuka biyu a Birnin Magaji a ranar Juma’a da rana, lamarin da ya sa mazauna yankin suka tsere zuwa bakin kogin da ke kusa, inda jirgin ruwa guda daya kawai ya kasance, kamar yadda mazauna yankin suka shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters.
“Babban ɗana da wasu ‘yan uwa biyu sun kasance cikin mutane 13 da suka mutu lokacin da jirgin ya cika da mutane fiye da kima,” in ji Shehu Mohammed, wani ma’aikacin lafiya a Birnin Magaji, a tattaunawarsa da Reuters.