Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta kafa kwamitin bincike kan hatsarin jirgin ƙasan Abuja-Kaduna

Kazalika Alkali ya ce kwamitin zai kuma ba shawara game da mafita na dindin da za ta hana sake aukuwar hatsarin.

Newstimehub

Newstimehub

28 Aug, 2025

9856451c3734259a73007a3c9125a066d36f4ebaeb4367b29f6e28fdff05c1a1

Ministan Sufurin Nijeriya, Said Alkali, ya kafa wani kwamitin bincike kan hatsarin jirgin ƙasan Abuja zuwa Kaduna da aka yi a garin Jere ranar Talata.

Wata sanarwa da daraktar watsa labarai ta ma’aikatar Sufurin, Misis Janet McDickson, ta fitar ranar Laraba a Abuja, ta ce kwamitin da ya ƙunshi masu ruwa da tsaki a lamarin zai binciki dalilan da suka janyo hatsarin.

Kazalika Alkali ya ce kwamitin zai bayar da shawara game da mafita ta dindindin da za ta hana sake aukuwar hatsarin.

Ministan ya ce kwamitin zai kuma ba da shawarwari game da yadda za a inganta sufurin jiragen ƙasa a Nijeriya.

Sanarwar ta ce ministan ya bayyana damuwa game da rashin aminci ga matafiya inda ya bayyana ‎daraktan da yake kula da ofishin babban sakataren ma’akatar sufuri Musa Ibrahim a matsayin shugaban kwamitin.