Sojojin Nijeriya sun ceto mutum 76 da aka sace a Jihar Katsina

Sojojin Saman Nijeriya ne suka samu wannan nasara a yankin Karamar Hukumar Kankara yayin wani aiki na yunkurin kamo wani shugaban ‘yan bindiga mai suna Babaro, wanda ake zargi da hannu a wani mummunan hari kan masallata a makon da ya gabata.

Newstimehub

Newstimehub

24 Aug, 2025

nigeria weapons 03364 main

Rundunar Sojin Sama ta Najeriya ta ceto mutum 76 da aka yi garkuwa da su, ciki har da mata da yara, bayan wani hari ta sama da sojojin suka kai kan maɓoyar ‘yan bindiga a Jihar Katsina da ke arewa maso yammacin Nijeriya, kamar yadda mahukunta suka bayyana a ranar Asabar.

Harin wanda aka kai a Tsaunin Pauwa da ke yankin Karamar Hukumar Kankara, na daga cikin yunkurin na kamo wani shugaban ‘yan bindiga mai suna Babaro, wanda ake zargi da hannu a wani mummunan hari da aka kai kan masallata a makon da ya gabata a garin Malumfashi da ke arewa maso yammacin Nijeriya.

Wani yaro ya rasa ransa yayin aikin ceton, kamar yadda ma’aikatar tsaron cikin gida ta jihar ta bayyana, amma ba a tabbatar da ko akwai wasu waɗanda suka jikkata daga cikin waɗanda aka ceto ko kuma daga cikin ‘yan bindigar ba.