Erdogan ya yi jimamin cika shekaru 26 da aukuwar girgizar ƙasar Marmara

Shugaban Turkiyya Erdogan ya yi addu’a ga mutanen da suka rasu sakamakon girgizar ƙasar Marmara ta shekarar 1999, mai ƙarfin maki 7.4, tare da sake miƙa ta’aziyyarsa.

Newstimehub

Newstimehub

18 Aug, 2025

27586f0973755dabc5ea2e1426fd043c735f4c750cb2d353cabd075b9cd45621

Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ranar Lahadi ya yi jimamin cika shekaru 26 da aukuwar girgizar ƙasar Marmara a shekarar 1999.

“Har yau, muna jin raɗaɗi a cikin zuciyoyinmu bisa rasa ‘yan’uwanmu a girgizar ƙasar Marmarai ta 17 ga watan Agustan 1999.