Babban Hafsan Tsaron Nijeriya ya kare yadda jami’an tsaron ƙasar suke tunkarar masu tayar da ƙayar baya da masu aikata laifi lamarin da wasu lokuta kan janyo mutuwar fararen-hula, yana mai cewa rundunar sojin na iya ƙoƙarinta wajen kauce wa rasa rayuka.
Sojin Nijeriya na ƙara amfani da hare-haren sama kan masu ɗauke da makamai a yankunan arewaci da tsakiyar ƙasar.
Kazalika rundunar sojin ta amsa kai hare-hare kan fararen-hula yayin fatattakar gungun ‘yan bindiga a arewa maso yammacin ƙasar, inda ake fama da rashin tsaro, kuma rundunar sojin ta yi alƙawarin gudanar da bincike kan waɗannan kura-kuran.
Babban Hafsa Tsaro, Janar Christopher Musa, ya kuma yi kira da a gyara dokokin ƙasa da ƙasa, yana mai cewa dokokin na takura wa dakarun ƙasar yayin da suka ƙyale ‘yan bindiga suna “kisa yadda suke so.”
A wata tattaunawa da bai saba yi wa manema labarai ba a babban birnin ƙasar Abuja ranar Laraba, Janar Musa ya ce rundunar sojin na yawan dakatar da ayyukanta domin hana cutar da fararen-hula, ko da ma yin hakan zai sa ta rasa damar da take da ita a fagen daga.