Ƙungiyar RSF ta Sudan ta kashe fararen hula 18 a yammacin Khartoum

Ƙungiyar RSF wadda ke rikici da sojojin Sudan ta kashe mutanen ne a wani hari da suka kai kan ƙauyuka biyu da ke yammacin Khartoum.

Newstimehub

Newstimehub

10 Aug, 2025

1754818985171 xaqi2 70b521da2ae9deec2a6ca194f15fb293fb63bb1a77cc8e7c1b0e7fc949f6925d

Ƙungiyar RSF ta Sudan ta kashe fararen hula 18 a wani hari da ta kai kan wasu ƙauyuka biyu da ke yammacin Khartoum a farkon makon nan, kamar yadda wata ƙungiya da ke sa ido ta tabbatar a ranar Asabar.

Dakarun ƙungiyar sun kai harin ne a ranar Alhamis a Jihar Kordofan ta Arewa, wanda yanki ne da ke da muhimmanci ga ƙungiyar ta RSF wurin fasa-ƙwaurin man fetur daga Libiya.

Yankin ya kasance babban fagen daga tsakanin sojoji da RSF tsawon watanni, kuma an katse duk wasu hanyoyi da jama’ar yankin za su sadu da sauran duniya waɗanda suka haɗa da wayoyi da intanet.
A cewar ƙungiyar kare hakkin ɗan adam ta Emergency Lawyers, wacce ta riƙa rubuta laifukan da ake aikatawa tun farkon yakin da aka fara fiye da shekaru biyu da suka wuce, harin da aka kai ƙauyuka biyu a Kordofan ta Arewa ya kashe fararen hula 18 tare da jikkata ɗaruruwa.

An kai wadanda suka jikkata zuwa babban birnin jihar, El-Obeid, domin samun magani.