Gwamnatin mulkin sojin Jamhuriyar Nijar ta sanar da ƙwace mahaƙar zinari ɗaya tilo a ƙasar, bayan da ta zargi kamfanin Australia da ke gudanar da ita da “manyan laifukan keta doka” a yayin da gwamnatin take neman karɓe ragamar harkokin ma’adanai na ƙasar.
Gwamnatin soji, wadda ta ƙwace mulki daga gwamnatin farar-hula a shekarar 2023, ta sha alwashin magance rashin tsaro da ya addabi ƙsar.