Ministan Harkokin Wajen Turkiyya, Hakan Fidan, zai kai ziyara zuwa Masar a ranar 9 ga watan Agusta don wata muhimmiyar ganawa ta diflomasiyya da za ta hada da ganawa da Shugaban Masar Abdel Fattah al Sisi, in ji majiyoyin diflomasiyyar Turkiyya.
Wannan ziyara na zuwa ne yayin da kasashen biyu ke bikin cika shekaru 100 na dangantakar diflomasiyya, kuma wannan ita ce ziyara ta biyu da Fidan zai kai birnin Alkahira a wannan shekarar, bayan halartar taron Ƙungiyar OIC da Ƙungiyar Ƙasashen Larabawa kan Gaza a ranar 23 ga watan Maris.
Ministan Harkokin Wajen Masar, Badr Abdelatty, ya ziyarci Turkiyya a ranar 4 ga watan Fabrairu, sannan ministocin biyu sun sake haduwa a watan Yuni yayin zaman Majalisar Ministocin Harkokin Wajen OIC karo na 51 a Istanbul.
Batun Gaza Na kan gaba
Tattaunawar a birnin Alkahira za ta mayar da hankali kan dangantakar kasashen biyu, ci gaban yankin, da kuma karfafa hadin kai mai fadi tsakanin Turkiyya da Masar.
Ana sa ran batun Gaza zai mamaye tattaunawar, inda bangarorin biyu za su yi musayar ra’ayoyi kan tattaunawar tsagaita wuta tsakanin Hamas da Isra’ila wadda Masar da Qatar da Amurka ke shiga tsakani, tare da tsara matakan tabbatar da isar da agajin jinƙai ba tare da tangarɗa ba.
Ana kuma sa ran Fidan zai jaddada cewa matakan Isra’ila na kawo cikas ga mafita ta samar da ƙasashe biyu, tare da bayyana cewa matakan kwanan nan na Isra’ila na mamaye Gaza su ne manyan kalubalen zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin.
Ministocin za su duba sakamakon taron kasa da kasa kan Falasdinu da aka gudanar a birnin New York daga 28 zuwa 30 ga watan Yuli tare da halartar Turkiyya, sannan su tattauna hadin kai wajen tallafawa sake gina Gaza — wani shiri da Turkiyya ta goyi baya a taron OIC da aka yi a Jeddah a farkon wannan shekarar.