Ɗaruruwan mutane, yawancinsu tsofaffin mata da masu goyo daga ƙauyen Jimrawa na ƙaramar hukumar Kaura Namoda na Zamfara, sun gudanar da zanga-zangar lumana ranar Alhamis a Gusau, babban birnin Jihar game da rashin tsaro a ƙauyensu.
Wannan na zuwa ne makonni biyu bayan mazauna ƙaramar hukumar Gusau ta jihar Zamfara suka yi zanga-zanga inda suka ce hare-haren ‘yan bindiga babu ƙaƙƙautawa sun kashe sama da mutum 100 a ƙauyukan da suka haɗa da Mada da Ruwan Bore da Fegin Baza da Lilo, da kuma Bangi.
Kaura Namoda da wasu ƙananan hukumomi a jihar Zamfara na fama da hare hare-haren ‘yan bindiga da suke kashe tare da garkuwa da gomman mutane inda suka lalata gidaje da dukiyoyin jama’a kuma suka raba mutane da muhallensu.
Jaridar Daily Trust ta Nijeriya ta ambato mazauna jihar na cewa rashin kyawun hanyoyin jihar na taimaka wa ɓarayin daji domin jami’an tsaro na fuskantar gagarumin ƙalubale wajen kai ga yankunan da lamarin ya shafa da wuri.
Sojojin Nijeriya sun tarwatsa bikin ‘yan ta’adda, sun kashe 30 a jihar Zamfara








