Ghana ta bai wa kamfanin MultiChoice wa’adi ya rage kuɗin kallo ga kwastamomi ko a dakatar da shi

Kamfanin MultiChoice wanda ya mallaki DSTV da GOTV, ya fuskanci matsaloli na shari’a a shekarun da suka gabata a ƙasashe da dama dangane da ƙarin farashi da saɓani kan haraji.

Newstimehub

Newstimehub

4 Aug, 2025

2025 07 23t080518z 674200674 rc2au5awi8xc rtrmadp 3 multichoice grp m a canal

Ghana ta bai wa kamfanin MultiChoice wanda ya mallakin DSTV wa’adin zuwa 7 ga Agustan 2025, domin sake nazari kan farashin da kwastamomi ke biya ko kuma fuskantar dakatarwa a ƙasar.

Ministan Sadarwa, Fasahar Dijital da Kirkire-kirkire, Samuel Nartey George, ya shaida wa majalisar dokokin ƙasar cewa dole ne kamfanin na Afirka ta Kudu ya aiwatar da ragin kashi 30 cikin ɗari na farashin dukkan tsarurruka na kallon talabijin da kwastamominsa ke amfani da su.

Sai dai George ya ce kamfanin MultiChoice bai bi umarnin rage farashin ba, inda ya bayar da dalilai daban-daban, ciki har da karyewar darajar kudin Ghana cedi da kashi 240 cikin ɗari a cikin shekaru takwas da suka gabata, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Ghana ya ruwaito.

George ya yi ikirarin cewa dalilan da MultiChoice ya bayar ba su da tushe, yana mai cewa yanayin tattalin arzikin Ghana ya inganta cikin watanni bakwai da suka gabata, wanda hakan ya sa ya dace a rage farashin biyan kuɗi.

‘Babu wani dalili’

Ya ce farashin biyan kuɗin kallon talabijin na MultiChoice a Ghana ya fi tsada idan aka kwatanta da sauran ƙasashen Afirka.

‘‘Abubuwa iri ɗaya ne, duk tsoffin fina-finan da ake nunawa iri ɗaya ne. Don haka, babu wani dalili da zai sa Ghana za ta fi tsada da kusan kashi 30 cikin ɗari,” in ji shi.

Ministan ya ce, a matsayinsu na masu kula da wannan fanni, ma’aikatar, ta hannun Hukumar Sadarwa ta Kasa (NCA), za ta yi duk abin da doka ta ba ta damar yi don kare masu amfani da kayayyakin Ghana ta ɓangaren “cazar kuɗi bisa rashin adalci” daga kamfanonin ƙasashen waje.

“Ba barazana nake wa MultiChoice ba, kuma ba na korar su. Muna kawai kare mutanen Ghana ne,” in ji shi.

MultiChoice, wanda ke samar da tashoshin kallo na talabijin inda ake biyan kuɗi a kalla a DSTV da GOTV, ya fuskanci matsaloli na shari’a a shekarun da suka gabata a ƙasashe da dama dangane da ƙarin farashi da saɓani kan haraji, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito.

A watan Yuli, Hukumar Kare Bayanan Sirri ta Nijeriya ta ci tarar MultiChoice naira miliyan 766 bisa zargin karya dokar ƙasar ta kare bayanai.

.