Brice Oligui Nguema, wanda ya jagoranci juyin mulki a Gabon a watan Agustan 2023, ya lashe zaɓen shugaban ƙasar na ranar Asabar da kashi 90.35 na ƙuri’un da aka jefa, a cewar Ministan Harkokin Cikin Gida wanda ya ambato sakamakon wucin-gadi.
A watan Agustan da ya gabata ne Nguema ya jagoranci juyin mulkin da ya kifar da Shugaba Ali Bongo, lamarin da ya kawo ƙarshen shugabancin iyalan Bongo na shekaru hamsin.
Tsohon janar na sojan ya shiga saƙo da lungu na ƙasar Gabon yana yaƙin neman zaɓe sanya da hular hana-sallah wadda ke ɗauke da taken “Tare Za Mu Gina Ƙasa”.
Ya yi alƙawarin inganta tattalin arzikin ƙasar ta hanyar faɗaɗa hanyoyin samun kuɗin shiga.