Turkiyya na son ƙarfafa yanayin miƙa ƙwarewarta a fannin makamashi ga Ethiopia tare da samar da haƙiƙanin ayyuka da kuma zurfafa haɗin kan da ke tsakanin ƙasashen biyu a fannoni daban daban, kamar yadda ministan makamashi da ma’adinan Turkiyya Alparslan Bayraktar ya bayyana ranar Talata.
Ma’aikatar makamashi da ma’adinan Turkiyya da ma’aikatar ruwa da makamashi ta Ethiopia sun rattaɓa hannu kan yarjejeniya ta haɗin kai a fannin makamashi wanda Bayraktar da ministan ruwa da makamashin Ethiopia Habtamu Itefa suka sanya wa hannu ramar Talata yayin ziyarar aikin Shugaba Recep Tayyip Erdogan zuwa Addis Ababa.
A ƙarkashin yarjejeniyar, ƙasashen biyu za su samar da ayyuka na hadin gwiwa fannonin lantarki da makamashin da za a iya sabuntawa da kuma inganta aiki da makamashi da kuma hadin kai wajen samarwa da kuma haɗa kayayyakin tashar samar da makamashi ta ruwa da kuma farfelun samar da lantarki.
Zuba jari na gwamnati da na ‘yan kasuwa cikin ayyukan samar da makamashi da samar da lantarki da dakon lantarki da kuma rarraba lantarki za su sami tallafi, kuma za a tabbatar da musayar ƙwarewa tsakanin hukumomi masu ruwa da tsaki.
“Muna da niyyar ƙarfafa musayar ƙwarewa da kuma samar da asalin ayyuka a fannoni daban daban daga samar da lantarki da kayayyakin aikin makamashi da zuba jari a makamashin da ake sabuntawa da kuma ayyukan samar da lantarki ta ruwa,” kamar yadda Bayraktar ya rubuta a kan kafar sada zumunta ta Turkiyya NSosyal.
“Mun cim ma yarjejeniya kan wani cikakken tsari na zurfafa haɗin kanmu da kuma aiwatar haɗin kai a sabbin ɓangarori daban daban daga makamashi da haƙar ma’adinai da ilimi da lafiya da sufuri da noma da muhalli da tsara birni da al’adu da kuma yawon buɗa ido,” in ji shihe added.














